Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya zargi tsohon mataimakinsa, Aminu Abdussalam, da kokarin kifar da shi domin ya karbi kujerar gwamna.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a Fadar Gwamnati yayin ganawarsa da mawaka, inda ya ce bai ma ga takardar murabus din tsohon mataimakin nasa ba, kuma babu wanda ya cutar da shi .
Jaridar Daily Trust ta ambato shi ya ce abin da ya faru wani yunkuri ne na kwace mulki, amma Allah bai bari ba.
Haka kuma, ya nuna damuwa kan yadda aka tafiyar da lamarin a cikin tafiyar Kwankwasiyya, yana tambayar dalilin da ya sa ba a bai wa tsohon mataimakin damar da yake nema ba.
Gwamnan ya kuma kare ficewarsa daga jam’iyyar NNPP, yana cewa matakin da ya dauka domin kare makomar al’ummar Kano ne, ba cin amanar jam’iyya ba.
Ya kara da cewa rashin tuntubar ‘yan Kwankwasiyya kafin daukar wasu muhimman matakai a jam’iyyar na daga cikin dalilan da suka sa ya fice.
A karshe, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na nan daram, tare da bayyana cewa akwai mutane masu cancanta da dama da ke neman cike gurbin mataimakin gwamnan da ya fice.
