DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeSiyasaShugaban APC na farko a jihar Jigawa ya fice daga jam’iyyar

Shugaban APC na farko a jihar Jigawa ya fice daga jam’iyyar

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na farko a jihar Jigawa, Ado Sani Kiri, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

Kiri, wanda ya taba wakiltar mazabar Ringim/Taura a majalisar wakilai tsakanin 2019 zuwa 2023, ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aike wa shugaban mazabar Kiri, mai ɗauke da kwanan wata 30 ga Maris, 2026.

A cikin wasikar, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari, yana mai cewa lokaci ya yi da zai janye daga harkokin jam’iyyar.

Ficewar tasa ta janyo muhawara a fagen siyasar jihar Jigawa, la’akari da rawar da ya taka wajen kafa tubalin jam’iyyar a jihar tun kafin zaɓen 2015.

Sai dai bai bayyana ko zai koma wata jam’iyya ba, lamarin da ke ƙara jawo hasashe kan matakinsa na gaba.

Masu sharhi na ganin wannan mataki na iya shafar haɗin kan jam’iyyar da ƙarfin ta a jihar Jigawa gabanin zaɓuɓɓuka masu zuwa a 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata