DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeBabban LabarinmuAtiku ya soki manufofin Tinubu kan rahoton bankin duniya

Atiku ya soki manufofin Tinubu kan rahoton bankin duniya

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan ƙaruwar talauci a Nijeriya, bayan sabon rahoton bankin duniya da ya nuna cewa kashi 63 bisa dari na ‘yan ƙasar na rayuwa cikin talauci.

Atiku ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a Abuja.

Ya soki manufofin tattalin arzikin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa wahalhalun da ake ciki na nuna gazawar tsare-tsaren gwamnati.

A cewarsa, cire tallafin mai da rage darajar naira cikin gaggawa ba tare da kyakkyawan tsari ga talakawa ba ne ya ƙara jefa jama’a cikin matsin rayuwa.

Ya ƙara da cewa hauhawar farashin abinci da kuma matsin da ƙananan ‘yan kasuwa ke ciki na nuna cewa manufofin ba su dace da halin da jama’a ke rayuwa ba.

Atiku ya buƙaci a sake fasalin manufofin tattalin arziki ta hanyar da za a mayar da hankali kan samar da ayyukan yi, inganta tsaron abinci da kuma kare jin daɗin al’umma.

Rahoton binciken wanda jaridar Punch ta ruwaito ya nuna cewa talauci ya ƙaru daga kashi 56 bisa 100 a 2023 zuwa 61 bisa 100 a 2024, kafin ya kai 63 bisa 100 a 2025, wanda ya kai kusan mutum miliyan 140.

Duk da raguwar hauhawar farashi, rahoton ya ce har yanzu tsadar rayuwa na ci gaba da ƙaruwa, lamarin da ke rage ƙarfin sayen kayan masarufi ga jama’ar kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata