An gaza cimma matsaya tsakanin Amurka da Iran bayan shafe sa’o’i 21 ana tattaunawa a birnin Islamabad na Pakistan, lamarin da ya jefa yarjejeniyar tsagaita wuta cikin rudani.
Rahoton Al Jazeera ya bayyana cewa mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, wanda ya jagoranci tawagar kasarsa, ya ce sun gabatar da shawara ta karshe amma ba a cimma matsaya ba kafin ya bar Pakistan.
A cewar bangarorin biyu, rashin cimma yarjejeniya a rana guda ba abin mamaki ba ne.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce tun farko ba a sa ran za a kammala komai cikin zama daya ba, yayin da kowanne bangare ke dora alhakin gazawar tattaunawar kan ɗayan.
