Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedAmbaliyar ruwa ta cinye wata makabarta a Borno

Ambaliyar ruwa ta cinye wata makabarta a Borno

 

Ambaliyar ruwa ta cinye wata makabarta yayin da wasu namun daji suka arce daga gidan zoo na Maiduguri jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta ba da labarin yadda aka wayi garin Talatar nan da ambaliyar a cikin birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

Rahotanni sun ce har namun dajin da ke gidan adana namun daji na Shehu Sanda Kyarimi sun arce, da bayanai suka ce akwai hatsari sosai tattare da kubcewar wadannan namun daji, musamman ga al’ummar da ke yankin.

Ruwan dai ya cike Maiduguri Bypass da hanyar gidan namun daji ta zoo road, har zuwa kwalejin koyon aikin kiwon lafiya ta College of Health Technology Maiduguri.

Baya ga wadannan wurare, bayanai sun kuma ce ambaliyar ruwan ta malaya har zuwa wata makabarta da kiristoci ke binne ‘yan’uwansu idan sun mutu ta wajen gidan Amb Baba Ahmad Jidda a tsohuwar GRA.

Kazalika, jami’ar Maiduguri ta UNIMAID ma ta sanar da dakatar da harkokin karatu har sai an ga abin da hali ya ba da. 

A cikin wata sanarwa daga magatakardan jami’ar Ahmad A Lawan, ta ce jami’ar ta yanke shawarar hakan, inda take jajanta wa malamai, ma’aikata da daliban jami’ar bisa wannan ibtilai da ya faru.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata