Friday, April 10, 2026
HomeUncategorizedFarashin litar fetur ya kai N1,200 a Kano

Farashin litar fetur ya kai N1,200 a Kano

Farashin litar man fetur ya daga zuwa sama, inda ya koma N1,200 a wasu gidajen mai a Kano, yayin da wasu gidajen mai mallakin kamfanin NNPC farashin ya koma N904.
Jaridar Daily Trust ta ba da labarin cewa yanzu haka layukan man fetur sun yi tsawo musamman a gidajen mai na NNPC biyo bayan samun labarin tashin farashin litar man.
Wani jami’i a wani gidan man NNPCL da ya nemi jaridar ta sakaya sunansa ya ce suna jiran umurni ne daga sama kafin su fara sayar da man a sabon farashi.
Sai dai wata takarda da DCL Hausa ba ta tabbatar da sahihancinta ba daga kamfanin NNPC ta ce har yanzu ba kamfanin bai ba da sabon umurnin sayar da fetur din a wannan sabon farashi.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata