Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedTsananin zafi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 47,000 a nahiyar...

Tsananin zafi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 47,000 a nahiyar Turai

 

Sama da mutane 47,000 suka mutu ta dalilin tsananin zafi a yankin Turai a shekarar bara 2023.

A wani bincike da cibiyar kula da yanayi da kiwon lafiya ta Barcelona ta fitar, ta ce kasashen kudancin Turai sun fi shafuwa da wannan matsala.

Binciken ya nuna cewa shekarar bara 2023, ita ce shekara mafi tsananin zafi da aka taba samu a tarihin baya-bayan nan.

Binciken da kamfanin Dillancin Labaran Reuters ya wallafa, ya ce a bara din, an samu sauyin yanayi da dumamar yanayi.

Kasashen Greece, Bulgaria, Italy da Spain ne kasashen da aka fi samun wadanda suka mutu ta dalilin tsananin zafin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata