An sassauta dokar hana fita a jihar Borno don gudanar da sallar Juma’a
Gwamnatin jihar Borno da hukumomin tsaro na jihar sun sassauta dokar hana fita da aka kafa a jihar daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3,domin ba da damar musulmai suje sallar Juma’a.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno ASP Nahum Kenneth Daso ANIPR, ya rabawa manema labarai , sanarwar tayi kira ga jama’a da su yi sallar Juma’a a masallatai dake kusa da su.
Sanarwar ta cigaba da cewa dokar zata ci gata daga karfe 3 na yammacin Juma’a zuwa karfe shida na safiyar ranar Asabar, bayan haka ana sa ran mutane za su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Tace hukumomin tsaro na jihar na neman hadin kan al’ummar don tabbatar da tsaron rayukan al’ummar jihar baki daya.

.jpeg)