DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Thursday, September 24, 2026
HomeSiyasa‘Ba za ka iya rufe min baki ba’ - Martanin Ireti Kingibe...

‘Ba za ka iya rufe min baki ba’ – Martanin Ireti Kingibe ga Wike

Sanata Ireti Kingibe, mai wakiltar Abuja a majalisar dattawa, ta mayar wa ministan Abuja, Nyesom Wike, martani, tana mai cewa ba zai iya tsoratar da ita ko hana ta magana kan al’amuran da suka shafi gwamnati ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito martanin Kingibe ya biyo bayan kalaman Wike na cewa ba za ta koma majalisar dattawa a zaɓen 2027 ba, yana mai cewa al’ummar Abuja sun zaɓi tsohon Sanata Philip Aduda domin ya sake wakiltarsu.

Wike ya yi kalaman ne a ranar Talata yayin duba ayyukan tituna da ake gudanarwa a Abuja, bayan da Kingibe ta zargi gwamnatin da karɓar wasu rance ba tare da amincewar majalisar dokoki ta ƙasa ba.

Ministan ya yi watsi da zargin, yana mai cewa kalaman sanatar sun nuna rashin fahimtar yadda ake samun rancen gwamnati, sannan ya ce Kingibe ba ta da abin da za ta ƙara wa al’ummar Abuja.

Sai dai a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X ranar Alhamis, Kingibe ta ce ba za ta bari zagi, barazana ko matsin lambar siyasa su hana ta gudanar da aikinta ba.

Ta ce aikinta a matsayin ‘yar majalisa shi ne yin tambayoyi, neman a yi wa jama’a adalci da kuma tabbatar da bin kundin tsarin mulki, tana mai cewa tambayar gwamnati kan rance da yadda ake kashe kuɗin jama’a ba rashin girmamawa ba ne.

Kingibe ta kuma ƙalubalanci Wike da ya fito da bayanan majalisar dattawa domin tabbatar da cewa an amince da rancen da ta yi tambaya a kansa, tana mai cewa a saninta, ba a taɓa gabatar da batun a gaban majalisar dattawa ba.

Ta ƙara da cewa babu wani minista ko jami’in gwamnati, komai matsayinsa, da ya fi ƙarfin doka ko kuma ya kamata a hana shi bincike da tambayoyi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata