Tuesday, April 7, 2026
HomeUncategorizedFarashin masara na cigaba da jijjiga aljihun talakan Nijeriya

Farashin masara na cigaba da jijjiga aljihun talakan Nijeriya

Farashin buhun masara mai cin tiya 40 na cigaba tashi a wasu kasuwannin sassan Nijeriya, inda a kasuwar Karamar Hukumar Gombi da ke jihar Adamawa da aka sai da N100-102,000, yayin da a makon jiya aka saya N87,000.

A jihar Lagos da ke yankin Kudancin Kasar Najeriya an sayi Buhunta N100,000 a makon karshe na watan Yunin 2024, haka nan batun yake a makon jiya.
To a kasuwar Mai’adua jihar Katsina dai farashin masara bai sauya zani ba ,an sayi buhunta N95,000 a makon jiya, hakan kuwa aka sai da a wannan mako.
Sai dai a kasuwar Dandume jihar Katsina an sayi buhun masara kan kudi N85-88,000 a makon nan.
N85,000 aka sayi buhun masara a kasuwar Dawanau da ke jihar a wannan makon da ke shirin kare wa, haka dai aka sai da a wancan satin.
Sai kuma kasuwar Giwa jihar Kaduna, inda aka sayi buhun masara N88,000 a satin nan, yayin da aka saya N86,000 a makon da ya gabata.
Sai kuma ɓangaren shinkafar Hausa da ta fi tsada a kasuwannin jihohin Kano da Kaduna da aka saya N155,000 a satin nan, amma a makon jiya N150,000 aka sayi buhun Shinkafar,
An samu ƙarin N5000 kenan a sati guda.
 A Mai’adua jihar Katsina an sayi shinkafar N14500,00 a makon nan, haka nan aka sai da a satin da ya gabata.
To a kasuwannin jihohin Adamawa da Lagos an sayar da buhun shinkafa ‘Yar gida N150,000 a satin nan, farashin dai bai sauya zani ba da na makon jiya.
Sai kasuwar Dandume jihar Katsina, an sayi buhunta N140-170,000 a satin nan.
Ita ma dai kasuwar Karamar Hukumar Girie N150,000 aka saya a makonni biyu da suka shude, haka kuma yake a wannan makon.
Shinkafar waje kuma ta fi sauki a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa da ake sayar wa N67,500.
Sai dai a kasuwar Giwa jihar Kaduna N88,000 ake sai da buhun a makon nan, yayin da a makon jiya aka saya N86,000.
Sai kasuwar Dawanau jihar Kano aka saya N87,000, bayan da a makon jiya aka saya N85,000, an samu karin N2,000 kenan.
To a kasuwar Dandume jihar Katsina an sayi buhun Shinkafar waje N78,000 a satin nan.
Sai kuma kasuwar Mai’adua jihar Katsinan aka sayi buhunta kan kudi N81,500, inda a makon jiya kuma aka saya N81,000.
A kasuwar Mile 12 International Market Lagos ana sai da buhun N80,000 a satin nan, yayin da a makon da ya wuce aka saya N83,000.
To idan muka leka bangaren farin wake ma dai farashin na ci gaba da tashi a sassan kasuwannin kasar musamman kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a kudancin kasar.
Inda aka sayi buhunta N250,000 cif a kasuwar Mile 12 International Market Lagos a makon nan, yayin da a satin da ya gabata aka saya N220,000, an samu karin N30,000 a mako ɗaya kacal.
Ita ma dai Kasuwar Dandume jihar Katsina an sayi Buhun N180-190,000 a makon nan.
Sai Jihohin Kaduna da Katsina da ake sayar da buhun farin wake N175,000 a makon nan, sai dai farashin ya bambanta a makon da ya gabata da aka saya N170,000 a kasuwar Mai’adua jihar Katsina.
N165-170,000 ake sayar da buhun farin wake a kasuwar Gombi jihar Adamawa a makon da ya gabata, haka batu yake a wannan makon.
 
A kasuwar Dawanau jihar Kano N178,000 aka sayi buhun wake a satin nan, yayin da a makon jiya aka saya N175,000.
Bari mu karkare farashin kayan abinci na wannan makon da Farashin Spaghetti.
N17,000 cif ake sai da kwalin taliyar a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a wannan satin, haka farashin yake a makon jiya.
Sai Mai’adua jihar Katsina da aka sayi kwalinta kan kudi N15,500 a wannan makon, amma a makon da ya gabata N150,000 cif ne kuɗinta.
Sai dai kwalin taliyar ya fi sauki a jihar Katsina a kasuwar Dandume na jihar da ake saidawa N14,500.
An sayi kwalin Spaghetti N13,700 a kasuwar Dawanau jihar Kano a makon nan, bayan da a makon da ya shude aka saya N13,500.
Ita kuwa kasuwar Giwa jihar Kaduna,N14,000 daidai aka sayi kwalin taliyar a wannan makon,haka nan aka saya a makon daya wuce.
N13,000 ake sai da kwalinta a kasuwar Zamani da ke jiya Adamawa a satin nan,bayanda a makon jiya aka saya N14,000 cif.
DCL Hausa A’isha Usman Gebi.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata