Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedZa a fara jigilar maniyyatan jihar Kano ranar Juma’a mai zuwa

Za a fara jigilar maniyyatan jihar Kano ranar Juma’a mai zuwa

Babban darakta a Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Baba Danbappa, ya ce za a fara jigilar maniyyatan jihar ranar Juma’a 24 ga watan Mayu, 2024.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka naɗa mataimakin Gwamnan jihar Kano, Commarade Aminu Abdussalam Gearzo a matsayin Amirul Hajj.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hakan yayin wani shiri na aikin hajji da aka gudanar a sansanin Alhazai yau Litinin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata