Wednesday, April 8, 2026
HomeUncategorizedMasara ta yi tsada a sassan jihar Lagos

Masara ta yi tsada a sassan jihar Lagos

Farashin kayan abinci na wannan makon a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, an saida buhun Masara N60,000 daidai a makon nan, bayan da makon da ya gabata aka sayar N58,000.
Masarar ta fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas, da aka saya N67,000, yayin da a makon da ya shude aka saya N65,000 an samu karin dubu 2000 kenan.
A kasuwar Mai’adua jihar Katsina, an sayar da buhun N64,000 a wannan satin, inda a makon da ya gabata aka sayar kan kuɗi N62,000.
Sai kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna da aka sai da buhun masara kan kudi ₦59,000 a makon nan, amma a makon jiya N57,000 aka sai da buhun.
To a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa masarar ta ɗan sauka, an sayi buhun N56-58,000 a makon nan, bayan da a makon da ya wuce aka sayar N57-60,000 cif.
Masarar ta fi sauki a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Nijeriya da aka saya N55,000 a makon da ke dab da ƙarewa, bayan da a makon da ya shude aka saida N57-60,000.
Idan muka je ga batun Shinkafar Hausa kuwa ta fi sauki a kasuwar Dawanau a da ke jihar Kano a makon nan, an sayi buhun Shinkafar Hausa N122,000, sai dai a makon jiya N118,000 aka sayar da buhun.
Sai dai fa, batun ya sha banban da kasuwar Mile 12 International Market Legos da aka sayar da buhun N142,000 a wannan makon, inda makon da ya gabata aka sayar N120,000 an samun karin kudi har N20,000 daidai a makon guda.
Sai kuma kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna da ke biye mata, inda aka sayar da buhun shinkafar Hausa N125,000, amma a makon jiya N120,000 ake sai da buhun, an samu karin N5000 kenan a makon guda kacal.
Shinkafar ta ɗan haure a kasuwar Girie da ke jihar Adamawa a wannan makon, da aka sayar N130,000, sai dai a makon da ya gabata kuwa an sai da N110,000, an samu karin N20,000 kenan a makon nan.
To a kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe kuwa kuɗin buhun Shinkafar Hausa bai sauya zani ba, inda aka sayi buhun N120-130,000, a makon da ya gabata, haka nan aka sai da a makon nan.
An sayi buhun Shinkafar Hausa N130,000 daidai a wannan makon, yayin da a makon jiya aka sayar N120,000 a kasuwar Mai’adua a jihar Katsina.
To a bangaren Shinkafar waje kuwa an sai da buhun kan kuɗi N75,000 a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano a makon nan, inda a makon jiya aka sai da N71,000.
A Mai’adua jihar Katsina, an sayi buhun Shinkafar Bature N68-69,000 a wannan makon, yayin da a makon jiya aka saya N62,000, an samu karin N7000 kenan kan farashin makon jiya.
An sayi shinkafar Bature N71,000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legos a satin nan, yayin da a makon jiya aka sai da N65,000.
Ita ma dai kasuwar Kashere da ke jihar Gombe N75,000 ake sai da buhun a makon nan da ke shirin karewa, bayan da aka saya N65,000 a makon da ya gabata, hakan ke nuni da cewa an samu karin N10,000 kenan a mako ɗaya .
N73,000 aka sayi buhun Shinkafa ‘yar waje a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa a satin nan, inda a makon da ya shude aka saya N55,000.
To bari ƙarƙare farashin shinkafar na wannan makon da kasuwar Giwa na jihar Kaduna, an sayar da buhun shinkafar waje N68,000 a satin nan, amma a satin da da ya wuce N65,000 ake sai da buhun.
Ga ma’abota cin alala da kosai kuwa, wake fari ya fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legos, da aka sai da N130,000 
Sai kasuwar Dawanau a jihar Kano a arewacin kasar, inda aka sayar da buhun N113-120,000 a kasuwar.
A Mai’adua jihar Katsina kuwa, an sayi buhun farin waken N117,000 a makon nan.
Da DCL HAUSA ta yi tattaki zuwa kasuwannin jihohin Gombe da Kaduna, ta taras da cewa ana sayen buhun farin waken kan kudi N107,0000 a kasuwar Giwa ta jihar Kaduna da kuma kasuwar Kashere da ke jihar Gombe.
Sai dai waken ya fi sauki a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa a wannan makon da aka sayar N90-95,000.
Bari mu kammala Farashin kayakin abinci na satin nan da farashin Kwalin taliyar Spaghetti.
A wannan makon da ke mana ban kwana dai, taliyar ta fi tsada a kasuwar Mai’adua jihar Katsina da sayar da kwalin N14,500, bayan da makon da ya shude aka saya N13,700.
Haka nan a wannan makon ma kudin kwalin taliyar N14,000 ne a kasuwannin jihohin Gombe da Kaduna, hakan kuwa aka sai da a makon da ya gabata ma.
A kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa an sayi kwalin taliyar N13,500 a makon nan, yayin da a makon jiya aka sai da kan kudi N13,000, cif cif.
N13,500 ake sai da kwalin taliya a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a makon nan, haka zancen yake a makon da ya gabata.
A kasuwar Dawanau da ke Jihar Kano N14,000 ake sayar da kwalin taliyar a makon da ya gabata, yayin da a wannan makon da ke dab da ƙarewa ake sayarwa kan kudi N13,000, an samu ragin N1000 guda kan farashin makon da ya gabata.
DCL HAUSA A’isha Usman Gebi.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata