Wednesday, April 8, 2026
HomeUncategorizedGwamnatin Nijeriya ta fara gyaran tsohuwar fadar shugaban kasa ta Dodan Barrack...

Gwamnatin Nijeriya ta fara gyaran tsohuwar fadar shugaban kasa ta Dodan Barrack da ke Lagos

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta sanar da fara gyaran tsohuwar fadar shugaban kasa da ke Dodan Barrack a birnin Lagos.

Gwamnatin ta ce tana da zummar kammala aikin gyaran nan da zuwa 29 ga watan Mayu mai zuwa, 2024 kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
Wani babban jami’in gwamnati da ke da hannu dumu-dumu a cikin aikin gyaran, ya tabbatar da cewa aikin ya zamo wajibi duba yadda ambaliyar ruwa ke barazana ga tsohuwar fadar shugaban kasar, inda har wasu wurare sun fara lalacewa.
Hakan na zuwa ne watanni 4 da shugaban kasa Bola Tinubu ya kasafta kashe Naira bilyan 4 don gyaran gidansa da ke Lagos da kuma gidan mataimakin shugaban kasa shi ma a Naira bilyan 3.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata