Wednesday, April 8, 2026
HomeUncategorizedMamakon ruwan sama ya lalata gidaje da dama a karamar hukumar Shanga...

Mamakon ruwan sama ya lalata gidaje da dama a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi

Nasir Idris

Ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar Kebbi ya lalata gidaje da dama a karamar hukumar Shanga ta jihar.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa mamakon ruwan  ya yi sanadiyyar  rugujewar gidaje masu tarin yawa a Garin Kestu na mazabar Atuwo a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi, tare Kuma da haddasa asarar dukiya ta miliyoyin Naira a yankin 

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya jajanta wa al’ummar Garin Kestu da ke unguwar Atuwo a karamar hukumar Shanga, tare da alkawarin tallafawa wadanda abin ya shafa.

Kamar yadda wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Ahmed Idris ya fitar, ta bayyana.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata