Thursday, April 9, 2026
HomeUncategorizedNatasha ta maka sanata Nwebonyi a gaban kotu kan zargin bata mata...

Natasha ta maka sanata Nwebonyi a gaban kotu kan zargin bata mata suna

 

Natasha Akpoti

Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta maka Sanata Onyekachi Nwebonyi a kotu tana neman diyya naira biliyan biyar bisa zargin bata suna da zarge-zargen da ke barazana ga martabarta.

Kotu ta karɓi karar ne bayan Sanata Nwebonyi ya yi wasu kalamai a taron manema labarai da Natasha ke zargin an taba kimarta a zarge- zarge marasa tushe, waɗanda suka shafi mutuncinta da rayuwarta ta siyasa.

Lauyan Sanata Natasha Michael Jonathan Numa, da ya shigar da karar, mai lamba Suit No: W/1359:25 a babbar kotun birnin tarayya Abuja ya ce kalaman sun janyo mata tozarta a idon jama’a kuma suna iya gurgunta aikinta a majalisa.

Sanata Nwebonyi bai mayar da martani ba tukuna, amma ana sa ran kotu za ta fara sauraron shari’ar nan ba da jimawa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata