DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jirgin yakin soji a Nijar ya yi hatsari

-

Ministan tsaron jamhuriyar Nijar ne janar Salifou Mody ya sanar da faduwar jirgin mai saukar angulu na dakarun kasar a yayin da yake kan hanyar sa ta dawowa daga wani aikin sintirin hadin gwiwa da askarawan Burkina Faso
Sanarwar ministan ta ce da misalin karfe 12 na ranar Juma’ar nan ce 5 ga watan Janairu ne hatsarin jirgin ya auku sakamakon matsalar na’ura a daidai lokacin da yake shirin sauka a filin jirgin sojoji na Kantchari
Babu wanda ya rasa rai dai a wannan hatsari amma sai karamin rauni da mutum daya ya samu kamar yadda sanarwar ta ambato

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan majalisar wakilai sun nemi gwamnatin tarayya ta gina sansanin sojoji a Yelwata da ke jihar Benue

Majalisar Wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kafa sansanin sojojin Nijeriya a garin Yelwata dake kan iyaka a karamar hukumar Guma...

Mun nemi INEC ta yi wa Tafiyar Matasa rijista a matsayin jam’iyyar siyasa da sunan “Access Party” – Bulama Bukarti

Jagoran Tafiyar Matasa, Barista Audu Bulama Bukarti, ya bayyana cewa sun mika bukatar yi wa tafiyar matasa rajista a matsayin jam'iyyar siyasa da sunan "Access...

Mafi Shahara