Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedGwamnatin Nijeriya ta karbi baƙuncin gimbiya Victoria ta kasar Sweden

Gwamnatin Nijeriya ta karbi baƙuncin gimbiya Victoria ta kasar Sweden

 

Victoria/Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya gana da Gimbiya Victoria, magajiyar sarautar kasar Sweden, wadda ke ziyarar aiki ta kwanaki uku a Nijeriya.

Ziyarar Gimbiyar na daga cikin matakan da ake dauka domin karfafa dangantakar diflomasiyya da tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Sweden.

A yayin taron, Shettima ya bayyana cewa Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa abokiyar kut da kut da Sweden, inda ya kara da cewa wannan ziyara za ta bude sabon babi na karfafa alaka tsakanin hukumomin kasashen biyu da kuma bunkasa musayar al’adu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata