Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedBabban Hafsan Sojin Kasa ya kai ziyara Plateau bayan harin da ya...

Babban Hafsan Sojin Kasa ya kai ziyara Plateau bayan harin da ya halaka mutane da dama

 

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Oluyemi Oluyede, ya kai ziyara zuwa karamar hukumar Bokkos a jihar Plateau, sakamakon harin ’yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 60.  

Janar Oluyede ya jagoranci tawagar manyan hafsoshin soji domin duba irin barnar da aka yi, ciki har da asarar rayuka da lalata dukiyoyin al’umma.  

Ana sa ran zai gana da shugabannin al’umma da na Fulani a yankin, tare da masu ruwa da tsaki, domin samun fahimtar juna da nemo hanyoyin magance rikice-rikice a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata