DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za’a ci gaba da amfani da tsaffin kudi har sai baba ta gani-Kotun Koli

-

Google search engine

Kotun Koli ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsaffin
takardun Naira kafada-da Kafada da tsaffin har sai baba ta gani, ma’ana babu
wata rana da aka sanya da za’a daina amfani da tsaffin kudi.

Kotun ta ce a yanzu bata amince a sanya wata rana da za’a daina
amfani da kudaden ba, har sai lokacin da gwamnatin tarayya ta samar da sabbin
dubarun sauyawa tsaffin kudin fasali ko kuma amfani da sabbi kadai, bayan taba
alli da masu tuwa da tsaki kuma kotun ta amince da tsarin, wanda dole ya
kasance ba zai cutar da ‘yan kasa ba.

Kotun mai alkalai shida karkashin
jagorancin mai shari’a Iyang Okoro ta yanke wannan hukunci ne bayan da
gwamnatin tarayya ta mika mata bukatar kara lokacin da za’a ci gaba da amfani
da tsaffin kudade.

Gwamnatin
tarayyar dai ta mika wannan bukata ne, bayan da ta ce ba zata iya buga sabbin
kudaden da zasu wadaci ‘yan kasa kafin nan da ranar 3 ga watan Maris da mai
zuwa ba, kamar yadda kotun ta tsayar a baya ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

INEC za ta fara sabuwar rijistar katin zaɓe daga ranar 18 ga Agusta a Nijeriya

Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta sanar da ranar 18 ga watan Agusta, 2025 a matsayin ranar da za ta fara sabuwar rijistar katin zaɓe a...

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Mafi Shahara