DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Fitacciyar ‘yar jarida kuma mai fafitika a shafukan sadarwa Samira Sabo, ta yi fatan ganin an saki hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum

-

‘Yar jarida a Nijar wacce ta yi fice a baya wajen sukar gwamnatin jamhuriyar ta 7 ta tsohon shugaban kasa Issoufou Mahamadou da magajinsa Mohamed Bazoum ta ziyarci gidan shugaba Issoufou Mahamadou domin taya shi murnar sakin abokan gwagwarmayar siyasarsa. 
Samira a cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce watanni biyu da suka gabata ta samu ganawa da tsohon shugaban kasar inda ta bukaci da ya shiga cikin lamarin siyasar kasar domin samar da mafita akan dambarwar siyasar da ake ke ciki.
‘Yar jaridar ta ce a nata ra’ayi, mataki na gaba ya kasance na sakin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum tare da tattaunawa da magoya bayansa har ma wadanda suke hijira a ketare.

Google search engine

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar wakilan Nijeriya ta amince wa Tinubu ya ciyo bashin dala biliyan 2.35

Majalisar wakilai ta Nijeriya ta amince da bukatar shugaban Tinubu na neman bashin dala biliyan 2.347 daga ƙasashen waje domin cike gibin kasafin kuɗin 2025...

Sojojin Nijeriya za su murƙushe ‘yan ta’addan Lakurawa — Babban hafsan sojin kasa Janar Waidi Shaibu

Babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Waidi Shaibu, ya sha alwashin murƙushe sabuwar ƙungiyar ‘yan ta’addan Lakurawa wadda ke addabar wasu sassan arewacin Nijeriya. Janar Shaibu,...

Mafi Shahara