DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Muna da bukatar Bruno Fernandes a Manchester United babu inda zai je – Rubin Amorim

-

Bruno Fernandes

Mai horar da kungiyar Manchester United Ruben Amorim ya shaida wa kyaftin din kungiyar Bruno Fernandes cewa ba zai je ko’ina ba duk da rahotannin yiwuwar komawarsa Real Madrid.

Google search engine

Tauraron dan kasar Portugal mai shekaru 30, wanda ya zura kwallaye 95 a wasanni 277 tun bayan komawarsa daga Sporting Lisbon a shekarar 2020, yana da kwantiragi a Old Trafford har zuwa shekarar 2027.

Sai dai a kwanakin baya an alakanta Bruno da komawa kungiyar Real Madrid da ke kasar Spain.

Sai dai kocin kungiyar Manchester United Rubin Amorim ya ce yana da bukatar Bruno a kungiyar saboda suna son sake lashe gasar Premier, don haka don haka suna da bukatar Ć™wararrun ‘yan wasa su ci gaba da kasancewa a Manchester United.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dattawan Nijeriya za ta tattauna da shugaba Tinubu kan kalaman Trump

Majalisar dattawan Nijeriya ta bayyana cewa za ta gana da shugaba Tinubu da bangaren zartarwa domin tattauna batun rikicin diflomasiyya da kalaman shugaban Amurka Donald...

ECOWAS ta yi watsi da zargin Trump na halaka mabiya addinin kirista a Nijeriya

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fitar da sanarwa mai dauke da watsi kan zargin cewa hare-haren ta’addanci da ke ƙaruwa a...

Mafi Shahara