DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeUncategorizedKungiyar Sanatocin Arewa sun yi Allah-wadai da kisan gillar matafiya-mafarauta a...

Kungiyar Sanatocin Arewa sun yi Allah-wadai da kisan gillar matafiya-mafarauta a Edo

Majalisar Dattawa

Kungiyar Sanatocin Arewa ta yi Allah-wadai da kisan mafarauta-matafiya da aka yi a Uromi, karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar Edo.

 A wata sanarwa da shugaban kungiyar Sanatocin Arewa, Abdulaziz Yar’adua ya fitar a Abuja, ‘yan majalisar sun bayyana lamarin a matsayin abu  ‘mai matukar tayar da hankali da bakin ciki.

A cewar sa  mafarautan  da suka tafi daga yankin Arewacin Nijeriya, an yi musu  kisan gilla na wulakanci, na ba gaira ba dalili  don haka sun yi Allah wadai da wannan danyen aikin, sun kuma yi kira ga gwamnatin Jihar Edo da ta dauki matakin gaggawa domin zakulo  batagarin  da suka aikata wannan kisan  tare da hukunta su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata