![]() |
| Bola Ahmad |
A ranar Asabar ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, zai cika shekaru 73 a duniya, zai hadu da ‘yan uwa musulmi a babban masallacin kasa da ke Abuja domin gudanar da addu’o’i na musamman ga kasar.
Bikin zagayowar ranar haihuwar Shugaba Tinubu dai ta zo ne daidai lokacin azumin Ramadan kuma ta zo ne watanni biyu kafin cikar gwamnatinsa shekaru biyu.
A cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban kasa shawara na musamman Bayo Onanuga ya fitar ta ce ana gayyatar al’umma domin yin addu’a ga kasa baki daya da kuma dorewar zaman lafiya a kasar.

