![]() |
| Bola Ahmed Tinubu |
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan kudirin dokar kafa hukumar raya yankin kudu maso yamma da Kudu maso kudu a matsayin doka.
Mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Kalu ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a ranar Laraba.
Benjamin yayin da yake jawabi ya bayyana cewa yana da tabbacin da hukumomin raya kasa za su yi tasirin wajen gudanar da gwamnati tun daga tushe.
Ya kuma yi godiya ga shugaban kasa bisa samar da hukumar a dukkanin yankuna shidda na kasar.

