DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeUncategorizedIran ta samu tikitin shiga gasar cin kofin Duniya ta 2026

Iran ta samu tikitin shiga gasar cin kofin Duniya ta 2026

Tutar Kasar Iran 

Bayan tashi wasa chanjaras biyu da biyu tsakaninta da Uzbekistan a filin wasa na Azadi da ke Tehran a Talatar nan, Iran ta samu tikitin shiga gasar cin kofin Duniya ta 2026.

Dan wasan Iran da ke taka leda a Intermilan, Mehdi Taremi, ne ya zura kwallaye biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a fafatawar, lamarin da ya baiwa tawagar ta Iran damar shiga gasar karo na hudu a jere, jimulla karo na bakwai a tarihi. 

Tawagar Uzbekistan ce ta fara jan ragamar wasan bayan da Dan wasa Khojimat Erkinov ya zura kwallo a minti na 16, sai dai Taremi ya sauya lamarin a minti na 52, yanzu haka dai Iran ita ce ta farko da maki 20 a rukunin A na gasar cancantar shiga gasar cin kofin Duniya a yankin Asia.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata