Friday, April 10, 2026
HomeUncategorizedSojin Sudan sun ce a ranar Asabar sun kwace wasu muhimman gine-gine...

Sojin Sudan sun ce a ranar Asabar sun kwace wasu muhimman gine-gine a tsakiyar birnin Khartoum daga hannun ‘yan dakarun sa kai na RSF

Sojin Sudan sun ce a ranar Asabar sun kwace wasu muhimman gine-gine a tsakiyar birnin Khartoum daga hannun ‘yan dakarun sa kai na RSF, a yayin da babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ya yi alkawarin samar da cikakken yanci ga kasar bayan kwato fadar shugaban kasa

Mai magana da yawun rundunar Nabil Abdallah ya ce sojojin na ci gaba da matsa kaimi ga dakarun RSF a fadin birnin, tare da ba da jerin sunayen gine-ginen da aka kwato ciki har da babban bankin kasar, hedkwatar hukumar leken asirin jihar da kuma gidan tarihin Sudan.

Sai dai duk da ci gaban da sojoji suka samu a babban birnin, kasar ta rabu gida biyu, inda sojoji ke rike da gabas da arewa yayin da kungiyar RSF ke iko da kusan dukkan yankin yammacin jihar Darfur da wasu sassan kudanci.

Masu fafutuka a ranar Asabar din nan sun ce an yi ajalin fararen hula da dama a wani harin da dakarun RSF suka kai a wani yanki mai nisa da jihar Darfur ta Arewa mai tazarar daruruwan kilomita daga babban birnin kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata