Friday, April 10, 2026
HomeUncategorizedSERAP ta maka Tinubu a kotu kan matakin da ya dauka na...

SERAP ta maka Tinubu a kotu kan matakin da ya dauka na dakatar da Gwamnn jihar Rivers, da ‘yan majalisar dokokin jihar

Bola Ahmed Tinubu/Sim Fubara

Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta maka shugaban kasa Bola Tinubu kotu kan dakatar da Gwamnan jihar Rivers Fubara da mataimakiyar sa na tsawon wata shida,abinda ta ce anyi shi ba bisa doka  ba.

SERAP ta yi zargin cewa matakin ya saba wa tanadin tsarin mulki da kuma bata tsarin mulkin dimokradiyyar Nijeriya.

Mambobin kungiyar a jihar Rivers su uku ne suka shigar da karar wacce  aka shigar gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Juma’a.

Daga cikin wadan da ake karar akwai babban lauyan gwamnati  kuma Ministan shari’a, Lateef Fagbemi SAN, da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya a matsayin wadanda ake tuhuma.

A cikin wata sanarwa da mataimakin darakta kungiyar Kolawole Oluwadare ya fitar a ranar Lahadi, ta bayar da hujjar cewa matakin na dakatar da zababben gwamnan da ‘yan majalisar jihar take hakkin jama’a ne.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata