DCL Hausa Radio
Kaitsaye

EFCC na binciken Mele Kyari kan badakalar matatun man Nijeriya

-

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci na binciken tsohon Manajan Daraktan kamfanin man Nijeriya NNPCL Mele Kyari da karin wasu mutane 14 bisa zargin karkatar da wasu makudan kudade da aka ware don gyaran matatun mai mallakin gwamnati a kasar.

Binciken ya mayar da hankali ne kan kudi Dala bilyan $2.896 da aka ware domin gyaran matatun mai a lokacin mulkinsu.

Google search engine

Matatun man su ne na Port Harcourt a jihar Rivers da aka ware wa Dala bilyan 1.56 bilyan, sai matatar man Kaduna da binciken da majiyar DCL Hausa ta Channels television ya gano an ware wa Dala milyan 740.6 da kuma matatar man Warri a jihar Delta da ita kuma aka ware wa Dala milyan 656.9.

Daga cikin muhimman abubuwan da aka gano har da gano makudan kudade a cikin asusun daya daga cikin shugabannin da aka kora, wanda ya kai kusan Naira bilyan 80, lamarin da ya haifar da karin bincike kuma ya kai ga kama dukkan shugabannin matatun mai guda uku da aka sallama aiki a kwanan nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara