DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

-

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su a ofishin ‘yan sanda na tsawon lokaci.

Sakin nasu ya zo ne bayan gabatar da su gaban alkali a kotun jihar Agadez a yau Juma’a, inda aka saurari batunsu bisa zargin da ake musu da kuma irin aikinsu na jarida.

Google search engine

Wannan na zuwa ne kasa da makonni biyu da aka gudanar da bikin ranar ‘yancin ‘yan jarida ta shekarar 2025, kan yadda hukumomin tsaro ke mu’amalantar ‘yan jarida a sassan duniya, musamman a yankunan da ke fama da rikice-rikice.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Wasu tsoffin ‘yan majalisar dokokin Kano sun yi mubaya’a ga Barau Jibrin a takarar gwamna a 2027

Wasu tsoffin 'yan majalisar dokokin jihar Kano da kuma masu ci a yanzu sun mara wa mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Barau Jibrin baya don...

Gwamnati ta binciki ta’azzarar matsalar tsaro a Nijeriya – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya ta da gudanar da bincike kan musabbabin ta'azzarar matsalar tsaro a wasu...

Mafi Shahara