Babban Bankin Duniya ya bayyana cewa kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL na biyan kaso 50% kacal na kudaden shiga da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur zuwa lalitar gwamnatin tarayya.
Wannan bayani na cikin sabon rahoton “Nigeria Development Update” da Babban Bankin Duniya ya fitar, inda aka nuna damuwa kan yadda ake gudanar da kudaden gwamnati da kuma rashin gaskiya a harkar kudaden shiga bayan cire tsarin tallafin man fetur.
A cewar rahoton, daga cikin Naira tiriliyan 1.1 da aka samu daga sayar da danyen mai da sauran hanyoyin samun kudin shiga a shekarar 2024, Kamfanin NNPCL ya biya Naira bilyan 600 kacal, inda ya bar gibi na naira biliyan 500 da ba a bayyana yadda aka yi da su ba.
