Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuAn kama iyalan rikakken dan bindiga Ado Aliero a Saudiyya

An kama iyalan rikakken dan bindiga Ado Aliero a Saudiyya

Hukumomin Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargin daya cikinsu ita ce mahaifiyar Ado Aliero, fitaccen shugaban ‘yan bindiga a Najeriya.

Majiyoyi sun ce jami’an leken asiri ne suka kama su a Madina, bisa zargin suna da alaka da masu ta’addanci daga Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ado Aliero na daga cikin manyan ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo kan laifukan garkuwa da mutane da hare-hare a Zamfara da makwabtanta.

RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata