Gwamnatin Nijeriya za ta cefanar da rukunin gidaje 753 da aka kwato daga hannun Emefiele
Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin sayar da gidaje 753 da aka kwato daga hannun tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, a matsayin dukiyar da aka samo daga laifi.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ma’aikatar gidaje da ci gaban birane, Salisu Haiba, ya fitar a Abuja ranar Talata.
Haiba ya bayyana cewa Ma’aikatar ta karɓi shaidar mallakar wurin mai dauke da rukunin gidaje 753 da hukumar EFCC ta kwato daga Emefiele.
Ya ce za a sayar da gidajen ga jama’a da kuma amfani da wasu don bukatu na musamman na gwamnati.
Daraktan ya ƙara da cewa shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede, ne ya mika takardar shaidar mallakar wurin ga Ministan gidaje da Ci gaban birane, Ahmed Dangiwa.
