Sanatocin jam’iyyar PDP reshen jihar Osun sun bayyana goyon bayansu ga shugaba Bola Tinubu domin ya yi tazarce a zaben 2027.
A wata sanarwar hadin gwiwa mai dauke da sa hannun Sanata Kamarudeen Oyewumi daga Osun ta Yamma, Sanata Olubiyi Ajagunla daga Osun ta tsakiya, da kuma Sanata Francis Fadahunsi,Osun Gabas, da suka fitar a ranar Talata sun bayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu da kuma ya sake yin wa’adi na biyu.
Hakan ya biyo bayan wani taro da aka yi a ranar Talata, inda Sanatocin suka goyi bayan shugaban kasar baki daya, inda suka bayyana irin nasarorin da ya samu a harkokin mulki, gyara tattalin arziki, da kuma samar da ababen more rayuwa a kasar.
Sun yaba da shirye-shiryen gwamnatin, tare da lura da ci gaban da ake samu a harkokin tsaron kasa da kuma raguwar farashin abinci, wanda suka bayyana a matsayin shaida na ingantattun manufofin shugaban.
