Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuZa mu tura Tinubu zuwa gida Lagos a 2027 - Malam Nasir...

Za mu tura Tinubu zuwa gida Lagos a 2027 – Malam Nasir El’rufa’i

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya sha alwashin cewa gamayyar jam’iyyun adawa za su kayar da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.

Da yake jawabi yayin wani taron Arewa Tech Fest karo na biyu da ya gudana a jihar Katsina, El-Rufai ya ce za su sauke Tinubu, yayin da za su ci gaba da aiki da Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani Bosun Tijani a gwamnati mai zuwa.

Tsohon gwamnan kuma jigo a jam’iyyar SDP ya ce Bosun Tijjani yana aiki mai kyau don haka za su ci gaba da aiki tare da shi.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata