Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci da rashawa ta yi karar babban bankin Nijeriya CBN akan rashin bayyana cikakkun bayanan kudaden da aka biya kai tsaye ga kananan hukumomi 774 a Nijeriya ciki har da kudaden da aka aike wa kowace karamar hukuma.
Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi.
Ya ce karar kungiyar ta biyo bayan wani hukunci da kotun koli ta yanke a watan Yuli, inda ta ce dole ne a biya kason kudaden da aka ware daga asusun tarayya da CBN kai tsaye ga kananan hukumomin da aka yi zabe, kuma babu wani gwamna da ke da ikon rikewa, sarrafawa ko amfani da kudaden da aka tanadar wa kananan hukumomin.
A cikin karar mai lamba FHC/L/MSC/521/2025 da ta shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Legas, SERAP na neman kotun da ta umarci CBN ya bayyana bayanan duk wani kudaden da aka biya kananan hukumomi 774 a Nijeriya ciki har da kudaden da aka aika wa kowace karamar hukuma tun bayan hukuncin kotun koli.

Hmmmm wani abu sai Kasata Nigeria, ai duk wanda yasan yanayin yadda Shari’a da kuma Al’amura ke tafiya a Nigeria, to zai san cewar Hukuncin da Kotun Koli ta yanke TATSUNIYA ce kawai. Shari’ar Kasar nan tafi yin Tasiri akan TALAKA ne