DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar NDLEA ta lalata tan 25 na miyagun kwayoyi a Kogi

-

NDLEA 

Hukumar hana da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya NDLEA reshen jihar Kogi ta lalata tan 25 na miyagun kwayoyi a Lokoja babban birnin jihar a ranar Laraba.

Google search engine

Wakilin shugaban hukumar NDLEA Brig. Janar Mohammed Buba Marwa a wajen taron, daraktan ayyuka da bincike na hukumar ta NDLEA, Ahmed Suleiman Ningi, ya jaddada illar da ke tattare da irin wadannan haramtattun magunguna.

Ya ce idan aka bari mutane na amfani da haramtattun magunguna irin haka,yana iya kara tsananta kalubalen tsaro a cikin kasar.

Kwayoyin da aka lalata sun hada da, Tramadol, Rohypnol, Diazepam, Exol-5, Pentazocine da  Cocaine.

Kwamandan hukumar NDLEA na jihar Kogi, Umah Mustapha Yahuza, ya bayyana cewa an kama motoci 24 na masu safarar miyagun kwayoyi tare da kwacesu. 

Ya bukaci hadin kan al’umma wajen yaki da fataucin miyagun kwayoyi, ya kuma bayyana cewa akwai karin tan biyar na haramtattun kwayoyi har yanzu ana ci gaba da shari’a akai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ghana ta sanya dokar fara koyar da yara a makarantu da harshen uwa

Gwamnatin Ghana ta sanar da sabuwar doka da ta wajabta amfani da harsunan uwa a yayin koyarwa a dukkan makarantun ƙasar, maimakon amfani Turanci. Ministan Ilimi...

Majalisar dokokin Nijeriya na shirin kirkirar sabbin jihohi da kananan hukumomi a fadin kasar

Majalisar dokokin tarayyar Nijeriya ta fara tattauna yiwuwar kirkirar sabbin jihohi 55 da kananan hukumomi 278 a fadin kasar.   Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa...

Mafi Shahara