Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuFadar shugaban Nijeriya za ta biyan tulin bashin Naira tiriliyan 2 na...

Fadar shugaban Nijeriya za ta biyan tulin bashin Naira tiriliyan 2 na lantarki da ake bin ta

Fadar shugaban kasa ta fara aiwatar da tsarin biyan basussukan da kamfanonin samar da wutar lantarki ke bin ta da ya kai Naira tiriliyan 2, nan da karshen rubu’i mai zuwa, a wani bangare na kokarin daidaita harkar wutar lantarki a Nijeriya.

Wakilin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin makamashi Eriye Onagoruwa ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wajen taron masu ruwa da tsaki na harkar samar da wutar lantarki karo na biyu na shekarar 2025, wanda hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya ta shirya.

Onagoruwa ya ce fadar shugaban kasa na son magance matsalar bashin da ya kawo cikas ga kamfanonin samar da lantarki wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata