Da alama dai rikicin na kunno kai a jam’iyyar APC mai mulki bayan amincewa da magoya bayan jam’iyyar APC suka yi na shugaba Bola Tinubu a watan da ya yi tazarce a karo na biyu a 2027.
A wani taro da shugabannin jam’iyyar suka shirya wanda ya samu halartar ‘yan jam’iyyar cikin harda shugaba Bola Ahmad Tinubu da sauran shugabanni a Nijeriya tare da amincewa da ya yi tazarce.
An bayar da rahoton cewa, hakan ya baiwa sauran ‘yan jam’iyyar kwarin guiwa, musamman ‘yan majalisar dokoki, da suka yi hasashen samun tikitin takara na yin tazarce a zaben 2027.
Hasashen da masu lura da al’amuran yau da kullum suka yi gargadin zai iya gurgunta tsarin dimokuradiyyar cikin gida idan ba a yi taka-tsantsan ba.
A Jihohi irin su Delta, inda Gwamna Sheriff Oborevwori da sauran ‘yan jam’iyyar PDP suka koma APC, tuni aka fara takun-saka kan yadda shugabannin jam’iyyar za su gudanar da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar kafin shekarar 2027.

Thank you so Much, I’m very interested and appropriate your work