Jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da rade-radin da ake ta yadawa na cewa shugaba Bola Tinubu na iya sauya mataimakinsa Kashim Shettima gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Jam’iyyar, ta bakin mataimakin shugabanta na kasa shiyyar Kudu maso gabas, Dr Ijeoma Arodiogbu, ta yi watsi da rade-radin, inda ta bayyana hakan a matsayin abu mai daure kai.
Inda ta ce wannan ba gaskiya bane domin akwai kyakkyawar alaka tsakanin Shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.
