Tuesday, April 7, 2026
HomeSiyasaAPC na cigaba da zawarcin Gwamnan Plateau na PDP

APC na cigaba da zawarcin Gwamnan Plateau na PDP

Kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC ta yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya ta sake jaddada kiran da take yi ga Gwamnan Jihar Plateau Caleb Mutfwang, da ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma APC, bisa umarnin shugabancin jam’iyyar na kasa.

Shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce kiran na da nufin karfafa jam’iyyar APC gabanin zaben 2027.

Saleh Zazzaga ya ce wannan kira da suke yi yana bisa umarnin da suka samu daga sama.

Sanarwar ta ce Gwamna Caleb Mutfwang mutum ne mai kishin cigaba, kuma suna da yakinin cewa ya dace ya kasance cikin babbar jam’iyyar APC.

Ya kuma gargadi shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Plateau da su guji nuna adawa da wannan yunkuri, yana mai cewa irin wannan adawa ba za ta haifar da da mai ido ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata