DCL Hausa Radio
Kaitsaye

SERAP ta yi karar babban bankin Nijeriya CBN kan karin kudin chaji na ATM

-

 

CBN

Google search engine

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Nijeriya ta yi karar babban bankin kasar CBN kan wasu sauye sauye na karin kudin cajin ATM da aka yi,da ta ce anyi shi ba bisa ka’ida ba.

A baya bayan nan ne dai CBN ya sanar da cewa, cire kudi a ATM din da ba bankin da mutum ke amfani da shi ba a yanzu za ta rika daukar naira 100 ga duk wanda ya ciri adadin kudin da ya kai naira dubu 20,000.

A karar da ta shigar mai lamba FHC/L/CS/344/2025 a ranar Juma’ar da ta gabata a gaban babbar kotun tarayya da ke jihar Legas, SERAP ta nemi kotun da ta yi duba kan matakin da CBN ya yanke na karin kudin cajin na ATM, wanda ta kira a matsayin rashin adalci, kuma ya saba wa tanadin dokar kasa.

SERAP na neman kotu da ta ba da sanarwar cewa matakin da CBN ya dauka na kara kudaden hada hadar kudi na ATM anyi shi ne ba bisa ka’ida ba, kuma ya sabawa tanadin sashe na 1 (c) da (d), 104, 105 da 127 (1) na dokar kasa ta tarayya da kuma kare hakkin al’umma ta 2018.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dalilin da ya sa muka maye gurbin rundunar Operation Safe Haven da Enduring Peace – Babban hafsan tsaron Nijeriya

Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Enduring Peace domin magance matsalar tsaro da ta...

Tsohon Sufeton ƴan sandan Nijeriya, Solomon Arase, ya mutu

Solomon Arase mai shekara 69 ya rasu ne a ranar Lahadi a asibitin Cedar Crest da ke Abuja, babban birnin tarayya.Wani ɗan uwansa ya tabbatar...

Mafi Shahara