Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuMijina (Sani Abacha) bai saci kudin Najeriya ba -Maryam Abacha

Mijina (Sani Abacha) bai saci kudin Najeriya ba -Maryam Abacha

Tsohuwar matar shugaban kasa, Maryam Abacha, ta musanta zargin cewa marigayi mijinta, Janar Sani Abacha, ya wawure dukiyar kasa.

A wata hira da aka watsa a tashar TVC don tunawa da shekaru 27 da rasuwarsa, ta ce kudin da ake kira “Abacha loot” ba sata ba ce, kuma ana bata masa suna ne kawai.

Maryam ta bukaci sahihin shaida daga masu zargi, tana mai cewa kudin da mijinta ya adana domin Najeriya sun bace bayan mutuwarsa.

Ta ce kabilanci da bambancin addini ke haddasa cin zarafinsa, kuma ta musanta cewa Abacha ne ya soke zaben 12 ga Yuni.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata