Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu ya jaddada cewa zai bada rayuwarsa ga jam’iyyar APC, musamman a jihar Abia.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa na Igbere a jihar Abia a jiya.
Tsohon gwamnan ya ce shi da ace sauran ‘yan jam’iyyar APC za su yi aiki tukuru don ganin shugaban kasa ya samu nasara a zabe mai zuwa da jam’iyyar ta kai ga nasara a ko ina a fadin kasar.
