An samu rikici a taron jiga-jigan jam’iyyar APC na Arewa maso Gabas a ranar Lahadi, bayan da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa a yankin, Comr Mustapha Salihu, ya kasa ambato sunan Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima yayin da yake bayyana goyon bayan sake tsayawa takarar Shugaba Bola Tinubu a karo na biyu.
An gudanar da taron ne a Jihar Gombe, inda kusan dukkan ministoci, ‘yan majalisa da gwamnonin jam’iyyar daga yankin suka halarta kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
