Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuShugaba Tinubu ne kadai zai iya zabar abokin takararsa a 2027 —...

Shugaba Tinubu ne kadai zai iya zabar abokin takararsa a 2027 — APC reshen Arewa ta tsakiyar Nijeriya

Jam’iyyar APC reshen Arewa ta tsakiyar Nijeriya ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne kadai ke da ikon zabar abokin takararsa a zaben 2027.

Wannan na zuwa ne bayan taron da jam’iyyar ta jam’iyyar Reshen Arewa maso Gabas ta gudanar a ranar Lahadi a Gombe, inda aka nuna goyon baya ga Tinubu, ba tare da ambaton mataimakinsa, Kashim Shettima ba.

Taron ya haifar da cece-kuce, inda wasu suka zargi cewa ana kokarin maye gurbin Shettima, musamman ganin yadda shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, da wasu shugabanni suka gaza ambaton sunansa a jawabansu.

Sai dai APC ta bayyana cewa goyon bayan da aka bai wa Tinubu ba ya da sharadi, kuma zaben Shettima a matsayin abokin takara ya rage ga Tinubu, kamar yadda jaridar Premium Times ta ayyana.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata