Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnonin Nijeriya za su dauki matakin magance yawan hauhawar farashi a kasar

Gwamnonin Nijeriya za su dauki matakin magance yawan hauhawar farashi a kasar

Gwamnonin jihohin Nijeriya 36 sun amince da rusa shingen kan tituna da kuma haraji da ake karba ba bisa ka’ida ba a fadin tarayya.

Gwamnonin sun yanke shawarar ne bayan taron kungiyar gwamnonin Nijeriya a Abuja wanda aka kammala da safiyar Alhamis.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya karanta sanarwar bayan taron, ya ce gwamnonin sun kuduri aniyar wargaza duk wasu baragurbin shingayen kan tituna da kuma haraji da ake karba ba bisa ka’ida ba wadanda ke haddasa tashin farashin abinci a kasar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata