Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuTinubu zai zabi abokin takararsa ne bayan babban taron APC – Fadar...

Tinubu zai zabi abokin takararsa ne bayan babban taron APC – Fadar Shugaban Kasa

Fadar shugaban Nijeriya ta ce Shugaba Tinubu zai zabi wanda zai yi masa takarar mataimaki a zaben shugaban kasa na 2027, bayan ya amince da takarar jam’iyyar a lokacin babban taronta a 2026.

Mashawarci na musamman ga shugaban kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust.

Da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa fadar shugaban kasa ta yi shiru yayin da ake ci gaba da samun cece-kuce kan batun cire mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima daga takarar Tinubu, Onanuga ya yi watsi da ikirarin cewa sun yi shiru ne saboda sun amince a sauya mataimakin shugaban kasar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata