Dr. Sam Amadi ya yi hasashen cewa Shugaba Tinubu na iya sauya Shettima da Kirista daga Arewa ta Tsakiya, a wani yunkuri na sassauta tasirin tsarin Musulmi-Musulmi da karfafa yankin da bai taba samun shugabanci ba tun 1999.
Jaridar Punch ta ruwaito masanin siyasar na cewa, alamu sun nuna sauyin yanayi a siyasar APC, inda Tinubu ke da tarihin sauya mataimaka tun lokacin da ya ke gwamnan Legas.
Hasashen na Amadi ya zo ne a daidai lokacin da ake rade-radin sabani tsakanin Tinubu da Shettima, musamman bayan an gaza ambato sunan Shettima a taron jam’iyyar APC da aka gudanar a Gombe lamarin da ya tada kura a kafafen siyasa.
