Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi tir da hari kan matafiya a Filato, tare da bai wa hukumomin tsaro umarnin gaggauta kamo duk masu hannu a laifin da ya kira tsantsar rashin imani.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce wajibi ne a kamo tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin don fuskantar hukunci.
Ya kuma bayyana lamarin a matsayin wani abu da ba za a laminta ba, inda ya bukaci gwamnatin ta Filato ta yi aiki da hukumomin tsaro don kawo karshen tashe tashen hankulan da ke faruwa a jihar.
