DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Farashin litar man fetur ya karu a gidajen mai mallakar NNPCL

-

Gidajen man fetur mallakin NNPCL sun yi gyare-gyare kan farashin man fetur, zuwa Naira 945 akan kowace lita a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin.

Haka kuma farashin ya ƙaru zuwa Naira 915 kowace lita a wasu gidajen man ta da ke Legas.

Google search engine

Karin ya nuna cewa an samu Naira 45 da Naira 35 ya karu a farashin baya a biranen Legas da Abuja.

Gyaran farashin dai ya zo ne kwanaki kadan bayan da matatar mai ta Dangote ta kara farashin man fetur daga Naira 825 zuwa Naira 880 kan kowace lita.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an fara amfani da sabon farashin a gidajen mai da dama mallakin kamfanin na NNPCL.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Muna da hujja ba a makance muke goyon Tinubu ba – Kungiyar Disciples of Jagaban

Kungiyar magoya bayan shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ta Disciples of Jagaban ta ce ba a makance ta ke nuna goyon baya ga shugaban ba,...

Rundunar sojin Nijeriya ta sulhunta kabilun da ke rikici a Taraba

By Salisu Ado Sulaiman Rundunar sojin kasan Nijeriya ta jagoranci zaman sulhu tsakanin kabilun da ke rikici a jihar Taraba. Kwamandan rundunar Operation Whirl Punch Brigadier Janar...

Mafi Shahara